Ana duba hanyoyin da za a bi domin tabbatar da cewa shirin aikin kidaya bai lalace ba.

Kwamishinan hukumar kidaya ta kasa mai kula da jihohin Jigawa da Kano, Alhaji Garba Zakar ya ce ana duba hanyoyin da za a bi wajen aikin kidayar jama’a na shekarar 2023 domin tabbatar da cewa shirin aikin bai lalace ba.

Daraktan hukumar na jihar Jigawa Ibrahim Iro ne ya bayyana haka a lokacin wani zaman ganawa kan aikin kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023 tare da manema labarai a Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Daraktan ya tabbatar da cewa dage aikin kidayar na shekarar 2023 zai haifar da sakamako mai kyau sabanin ra’ayin cewa dage aikin na iya kawo cikasa ga nasarar gudanar da shi.

Ibrahim Iro ya ce hukumar ba wai kawai tana duba bukatar gaggawar gabatar da aikin kidayar jama’a mai zuwa ba ne, amma ta fi damuwa da kafa ginshikin ayyukan kidayar da za ayi a gaba. Ya kuma bayyana cewa hukumar ta samu na’urorin aikin kidayar shekarar 2023, inda ya kara da cewa na’urorin akalla dubu 500 an kai su jihohi 36 da birnin tarayya bayan an saita su.

Comments (0)
Add Comment