Hukumar kidaya ta kasa NPC ta sanar da yiwa yara fiye da miliyan 10 rijistar haihuwa cikin watanni 3 da suka gabata, alƙaluman da ke tabbatar da tagomashin da ƙasar mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika ke gani ta fuskar ƙaruwar al’ummarta.
Shugaban hukumar ta NPC Alhaji Nasir Isa Kwara da ke sanar da wannan alƙaluma yayin jawabinsa gaban manema labarai bayan ziyarar da mai ɗakin shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu ta kai tare karrama jaririn farko da aka haifa cikin shekarar nan a asibitin Asokoro da ke Abuja, ya bayyana cewa ana samun karbuwar yiwa jarirai rijista a sassan kasar.
Shugaban wanda ya samu wakilcin kwamishinan ayyuka na hukumar daga jihar Katsina ya bayyana cewa hukumar NPC na aiki tuƙuru wajen ganin kowanne jariri ya samu rijistar haihuwa da zarar an haife shi a ko’ina ya ke a sassan kasar.
Sai dai jami’in na NPC ya bayyana cewa a yanzu sun fi mayar da hankali kan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 da ba a samu damar yi musu rijista ba.