An yi hasashen zazzafar rana da kuma tsawa daga yau Litinin zuwa ranar Laraba

Hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi hasashen zazzafar rana da kuma tsawa daga yau Litinin zuwa ranar Laraba.

Hasashen yanayin da Hukumar NiMet ta fitar jiya Lahadi a Abuja ya yi hasashen yanayi mai tsananin rana a sassan jihohin Yobe da Borno a yau Litinin, tare da yiwuwar tsawa a wani bangare na Kebbi.

A cewar NiMet, sauran sassan Arewa zasu su kasance cikin rana tare da gajimare a lokutan safiya. A wannan rana, ana sa ran za a yi rana a wasu sassan jihohin Bauchi, Taraba, da Kaduna.

Comments (0)
Add Comment