Rahotanni na cewa an yi garkuwa da wani ɗansanda mai suna Modestus Ojiebe wanda ke aiki da rundunar ƴansandan jihar Kwara, a babban titin Kubwa da ke cikin birnin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito daga masanin harkokin ƴanbindinga, Zagazola Makama da ma wasu majiyoyi daga cikin ƴansandan cewa lamarin ya auku ne a kusa da unguwar Dei-Dei gab da barikin ƴansanda da ke Abuja.
“Lamarin ya auku a daidai lokacin da ya tsaya domin ya duba motarsa da ta lalace, sai wasu mutane suka zo a mota, suka ƙwace masa wayoyi da na matarsa. Da suka gane ɗansanda ne sai suka saka shi a motar suka tafi da shi, suka bar matar da motar.”
Sai dai an ce ƴansanda sun baza jami’ansu, domin suke binciken masu wucewa da motoci da zimmar ceto abokin aikin nasu.
Sai dai an yi yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansandan Abuja, Josephine Adeh, amma haƙar ba ta cimma ruwa ba.