An yankewa tsohon shugaban harkokin tsaron ƙasar Saudiyya hukuncin ɗaurin shekaru 20

Kotu a kasar Saudiyya ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 20 a kan tsohon shugaban harkokin tsaron ƙasar kan laifukan Rashawa.

Haka kuma kotun ta ci tarar Janar Khalid Bin Qarar al-Harbi, dala dubu 250,000 tare da umartarsa ya maido da kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 3.5 na rashawa da ya wawushe.

An samu tsohon jami’in – da ya riƙe wannan muƙami a ma’aikatar tsaro na tsawon shekaru shida – da laifukan zamba da karɓar kuɗaɗen da  kuma amfani da muƙaminsa wajen biyan buƙatun kansa.

Hukuncin shi ne na ƙarshe kuma babu damar daukaka kara. 

Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta jaddada kudurin gwamnatin ƙasar na ci gaba da yaƙi da duk wani nau’in cin hanci  a kasar.

Comments (0)
Add Comment