An umarci kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja da ya biya wasu al’ummomi diyya

Hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta kasa ta umarci kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja da ya biya diyya ga wasu al’ummomi a Kogi da Abuja sakamakon rashin aikin yi.

A cewar takardar da  hukumar ta fitar a ranar Alhamis, yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Wuse, Garki, Asokoro, da kuma Ajaokuta a Lokoja, jihar Kogi.

Wadannan yankunan sun fuskanci karancin wutar lantarki tsakanin 1 zuwa 25 ga Agusta, 2024, duk da cewa suna kan Band A.

A cewar hukumar, duk wani mai amfani da wutar da ya kasa cika sa’o’in da ake bukata na tsawon kwanaki bakwai a jere, za a rage masa kudin wutar, kuma dole ne a biya  shi diyya.

Comments (0)
Add Comment