An samu nasarar dakile wani yunkurin juyin mulki da ya nufaci hambarar da gwamnatin Kyaftin Traore

Burkina Faso ta sanar da dakile wani yunkurin juyin mulki da ya nufaci hambarar da gwamnatin Kyaftin Ibrahim Traore, kusan shekara guda bayan jagoran ya karbi ragamar kasar a wani juyin mulki da ya jagoranta.

Wata sanarwa da Burkina Faso ta rabawa manema labarai, ta ce a ranar 26 ga watan da muke ciki na Satumba ne wasu sojojin da ke sashen tattara bayanan sirri na kasar suka yi yunkurin juyin mulkin amma aka yi nasarar dakile shi.

Sanarwar wadda kuma aka karanta ta kai tsaye ta gidan talabijin, ta ce tuni aka kame sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin tare da masu taimaka musu.

Sanarwar ta ce manufar masu juyin mulkin shi ne jefa Burkina Faso a tashin hankali kari kan matsalolin tsaron da suka dabaibayeta.

Yunkurin juyin mulkin dai ya zo na kasa kwanaki 5 gabanin cika shekara guda da juyin mulkin da ya kai Ibrahim Traore ga samun jagorancin kasar wanda ya gudana a ranar 30 ga watan Satumban 2022.

Juyin mulkin na Traore dai shi ne na biyu da Burkina Faso ta gani cikin watanni 8 a bara, wanda ya hambarar da kujerar Paul-Henri Sandaogo Damiba wanda ya yi wa gwamnatin Rock Marc Christian Kabore juyin mulki sakamakon tabarbarewar tsaro a karuwar ayyukan ta’addanci. A Talatar da ta gabata ne dubunnan ‘yan Burkina Faso suka gudanar da wata zanga-zangar nuna goyon baya ga kyaftin Traore a birnin Ouagadougou tare da neman sojojin su dauki matakin bai wa shugabancin nasa kariya, bayan fitar wasu jita-jita da ke sanar da yiwuwar yi wa shugaban juyin mulki.

Comments (0)
Add Comment