Hukumar kula da makarantun yayan Fulani makiyaya ta jihar Jigawa ta samar da kayayyakin koyo da koyarwa ga makarantun yayan Fulani makiyaya na kananan hukumomin Ringim da kuma Taura
Jamiin Hukumar mai kula da shiyyar Ringim Mallam Uba Chiroma ya bayyana hakan ga jamiin yada labarai na yankin
Yace an raba kayayyakin koyo da koyarwar ne ga makarantun Duguwa da Kauye Waziri da Takai da kuma Eddowa.
Sauran sun hadar da Wadugur da Daneji Fulani da Se Kukuwa da Sabon Sara. Ya bukaci iyaye fulani dasu kara kaimi wajan tura yayansu makararnta domin samun ilmin boko dana arabiyya.