An roƙi Joe Biden da yasa baki Najeriya ta saki jami’in Binance

Wakilan Majalisar Dokokin Amurka 16 sun roƙi Shugaba Joe Biden da ya shiga tsakani don ganin an saki babban jami’in kamfanin hada-hadar kuɗin intanet, Binance, Tigran Gambaryan, wanda ake tsare da shi a Najeriya tun a watan Fabarairu.

Gwamnatin Najeriya ta kama Gambaryan inda yake fuskantar tuhumar ƙin biyan haraji da kuma yadda kamfanin ke taimaka wa masu hada-hada wajen kauce wa haraji.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ƴan majalisar sun ce a matsayin Gambaryan na ɗan Amurka, bai dace gwamnatin wata ƙasa ta tsare shi ta hanyar da ba ta dace ba, har ma a riƙa gallaza masa.

Ƴan majalisar sun kuma bayyana damuwarsu kan lafiyarsa.

‘Yan majalisar sun ce suna buƙatar taimakon gwamnatin Biden domin mayar da Gambaryan ƙasarsa.

Comments (0)
Add Comment