An rantsar da sabbin shugabannin kananan hakumomi a Jihar Jigawa

Gwamna Umar Namadi ya rantsar da sabbin zababbun shugabannin kananan hakumomi da aka zaba a karshen makon daya gabata.

An gudanar da rantsuwar ne a safiyar yau litinin a gidan gwamnati dake Dutse babban Birnin Jiha.

Gwamna Umar Namadi ya bukaci sabbin shugabannin kananan hakumomin su kasance masu gaskiya da rikon amana yayin wa’adin mulkin su.

Hakumar zaben dai ya ayyana yan takarkaru 27 na jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka yi nasara a zaben na ranar Asabat, abinda ke nuna cewa jam’iyya mai nulki ce keda dukkan kejerun sahugabannin kananan hakumomi da ake dasu a jiha.

Can a cikin labaran mu na yammaci dama sauran shirye-shiryenmu zamu kawo muku karin bayani.

Comments (0)
Add Comment