Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Baduru Abubakar ya rantsar da sabon babban Khadin Jihar tare da karin wasu alƙalan manyan kotuna a fadar gwamnatin jihar a jiya.
Da yake magana a wurin taron da aka yi shi ba tare da cikowar jama’a ba saboda halin da ake ciki na bukatar karancin cunkoso da bayar da tazara, Gwamna Badaru bukaci sabbin masu Shari’ar da su ji tsoron Allah yayin da suke aiwatar da aikin su.
Kwamishinan Shari’a na jihar Dr. Musa Adamu Aliyu ne ya jagoranci rantsuwar sabbin alƙalan biyu da kuma babban Khadin.
- Gwamnan jihar Kano zai bayar da N670M domin yaki da matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar
- Ganduje ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu
- Kotu ta umarci a gabatar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Kore, Bello Bodejo, a gabanta
- Sojin Najeriya na samun gagarumin ci gaba wajen yaki da satar man fetur a yankin Neja Delta
- Mutane da dama sun mutu bayan da wani jirgin sama ya yi hatsari a Kazakhstan
Alƙalan manyan kotunan su ne mai shari’a Musa Ubale da mai shari’a Husseina Aliyu Adamu sai kuma Khadi Muhammad Sani Salihu.
Taron rantsuwa ya samu halartar mataimakin gwamna Malam Umar Namadi da kakakin majalisar dokoki ta jihar Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini.