An rantsar da Aisha Iliyasu Abubakar a matsayin shugabar kungiyar NAWOJ reshen Jihar Jigawa

Shugabar kungiyar NAWOJ ta kasa, Ladi Bala, ta rantsar da Aisha Iliyasu Abubakar a matsayin shugabar kungiyar NAWOJ reshen Jihar Jigawa na tsawon shekaru uku.

Rantsuwar ta gudana ne a dakin taro na Maryam Sani Abacha women’s center dake birnin tarayya Abuja, inda Aisha Iliyasu Abubakar ta karbi rantsuwar a matsayin shugabar kungiyar, sai kuma Salamatu Nuhu da aka rantsar a matsayin Sakatariyar kungiyar a jihar Jigawa.

A ranar 1 ga watan Nuwambar 2023 ne aka gudanar da zaben kungiyar wadda Aisha Iliyasu ta samu nasarar zama zababbiyar shugabar kungiyar. Sauran masu rike da mukaman kungiyar sun hada da Bushira Muhammad mataimakiya, sai kuma Maryam Ibrahim mataimakiyar Sakatariya, da Aisha M. Sani mai rike da mukamin Ma’aji.

Comments (0)
Add Comment