Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Jigawa ta bada gudunmawar buhunan masara 260 ga wadanda suka gamu da ambaliyar ruwa a garuruwan Shungurum da Gangara da Babaldu da Argun da Malamawa da kuma Kuja dake yankin Karamar Hukumar Birnin-Kudu.
Sakataren zartarwar hukumar, Yusuf Sani Babura, ya sanar da haka lokacin rabon kayan a garin Babaldu.
Da yake jawabi, Yusuf Sani Babura yace bugu da kari, hukumar ta bada tallafin buhunan garin kwaki 50 da na sikari 7 ga wadanda iftila’in ya shafa. Sani Babura ya ce an bayar da tallafin ne domin rage musu radadin rayuwa da suke fuskanta.