Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ne ya amince da nadin kuma ya bayyana cancantar Farfesa Jiddere da jajircewarsa ga harkokin Arewa.
Shugaban Hukumar Gudanarwa ta kungiyar, A. M. Al-Amin Daggash mai ritaya, a cikin wata sanarwa ya bayyana Farfesa Jiddere a matsayin fitaccen mai dabarun koyarwa kuma mai kwarewa da kwazo.
Jiddere ya maye gurbin Abdul-Azeez Suleiman, wanda yanzu yake aiki a matsayin Darakta na kungiyoyi masu zaman kansu da kuma na fafaren hula na kungiyar dattawan Arewa.
Farfesa Jiddere, a jawabinsa na karbar nadin, ya nuna jin dadinsa da nadin da aka yi masa, tare da tabbatar da aniyarsa ta cimma manufofin kungiyar dattawan Arewa.