An mikawa hukumar NDLEA jakunkuna 72 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 40

Rundunar sojin ruwan Kasar nan  ta bayyana cewa ta mikawa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) jakunkuna 72 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 40 tare da wasu mutane hudu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi. 

Kwamandan Rundunar, Commodore Rafiu Oladejo wanda ya samu wakilci a wajen bikin mika kayayyakin da babban jami’in sojin ruwa, Kyaftin Mutalib Raji ya bayyana cewa jami’an rundunar sojin ruwan ne suka kama kayan a ranar lahdi.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Hussaini Ibrahim ya fitar, ya ce hakan ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu kan wasu muggan laifuka da ke faruwa a kusa da bakin tekun Lekki a jihar Legas.

Ya kuma gargadi masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da su guj aikata irin wadannan ayyuka.

Comments (0)
Add Comment