Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC ta karɓi ƙorafi daga wasu daga cikin mutanen yankin Kogi ta Tsakiya, inda suke buƙatar hukumar ta shirya musu zaɓen kiranye ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa ta Najeriya.
Wata mai suna Charity Ijese ce ta miƙa ƙorafin a madadin ƴan mazaɓar a ofishin hukumar da ke birnin Lokoja a jihar Kogi, sannan babbar sakatariyar hukumar a jihar, Mrs. Rose Anthony ta karɓa ƙorafin a hukumance.
A cikin takardar ƙorafin, sun rubuta cewa, “mu da muka sanya hannu a wannan ƙorafin halastattun masu kaɗa ƙuri’a ne a mazaɓar Kogi ta Tsakiya, don haka muke so mu yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba mu dama.”