Hukumar Shari’a ta Jihar Jigawa ta kori wani Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci, Safiyanu Muhammad, saboda karbar cin hancin Naira dubu 50 daga hannun wani mai kara.
Duk da cewa daraktan yada labarai na ma’aikatar shari’a ta jihar, Abbas Rufa’i, bai fayyace yanayin saba dokar da alkalin ya aikata ba, amma manema labarai sun tattaro cewa an bincike shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu bayan da mai kara ya shigar da kara a gabansa kan karbar cin hanci naira dubu 50.
Sai dai hukumar ta gargadi ma’aikatan ta da su guji duk wani nau’i na cin hanci da rashawa domin tsaftace bangaren shari’a.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa hukumar ta sake jaddada aniyar ta na daukar mataki kan duk wani ma’aikaci da aka samu laifin cin amana.
Kazalika Sanarwar ta ce, an yanke hakuncin ne yayin taro karo na 170 na hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar jigawa da aka gudanar a birnin Dutse a ranar Alhamis da ta gabata.