Jami’ai a Mozambique sun ce fiye da kaji 45,000 aka kashe, aka kuma ƙona tare da binne su a kudancin kasar domin daƙile yaɗuwar cutar murar tsuntsaye a ƙasar.
An shigar da kajin ne daga makwabciyarta Afrika ta Kudu, inda cutur murar tsuntsaye ta ɓarke.
Cutar ta yaɗu zuwa gundumar Morrumbene da ke kudancin lardin Inhambane na Mozambique.
Hukumomi na ƙoƙarin daƙile cutar, yayin da fargaba ke ci gaba da bazuwar cutar zuwa wasu sasan ƙasar.
Murar tsuntsaye, cuta ce da ke kama kaji da sauran tsuntsayen daji.
Cutar kan yaɗu ta hanyar cuɗanya da tsuntsayen gida cikin kwanaki, ta hanyar kashi da yawun tsuntsayen da suka kamu, ko ta hanyar cin abinci ko shan ruan da suka gurɓace.