Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai kan sojojinta a jihar Borno.
A wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya ce an kashe sojoji guda shida, sannan wani kwamandan ƴan sa-kai ya jikkata.
Sai dai Buba ya ƙara da cewa a gumurzun, sojojin sun samu nasarar kashe ƴan Boko Haram 34, sannan sun ƙwato wasu makamai.
Wannan ne karo na biyu a cikin wata biyu da mayaƙan Boko Haram suka kashe sojoji a Najeriya. A watan Nuwamban 2024, an kashe gomman sojoji a wasu hare-hare da mayaƙan suka kai kan sojoji a ƙauyen Kareto da ke ƙaramar hukumar Mobbar da ke jihar Borno.