Rundunar sojin Isra’ila ta IDF ta tabbatar da mutuwar sojanta na farko tun bayan da ta ƙaddamar da shirinta na kutsawa cikin Lebanon ta ƙasa.
Rundunar IDF ta ce an kashe mata soja mai muƙamin kyaftin masi suna Eitan Yizhak Oster mai shekara 22 a cikin Lebanon ɗin a ranar Laraba.
Matashin sojan shi ne kwamandan sashen Egoz, sashe na musamman da suka ƙware wajen yaƙin sari ka noƙe.