Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun kai hari tare da kashe wani DPO na ƴansanda a karamar hukumar Ughelli ta Arewa da ke jihar Delta.
Mai magana da yawun ƴansandan jihar, Bright Edafe, shi ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce ƴan bindigar sun kuma raunata wani DPO na shiyyar Ororoekpe inda aka garzaya da shi asibiti domin ba shi kulawa.
Edafe ya ce jami’an ƴansandan biyu sun fita samame ne da wasu jami’ai lokacin da ƴan bindigar suka yi musu kwantan-ɓauna, inda ya ce ana ci gaba da bin sawunsu da nufin kama su.
Kakakin ƴansandan ya kuma ruwaito karya doka da oda a wata karamar hukumar Aniocha ta Arewa na jihar inda matasa suka far wa kayayyaki tare da cinna musu wuta.
A cewarsa, tarzomar ta ɓarke ne bayan lakaɗawa wani mutum duka har ta kai ga mutuwarsa da wani yayi wanda suke zargi da kwace filayen al’umma a yankin.
Wasu jagororin al’umma sun nuna adawa da matakin abin da ya janyo tarzomar da ta yi sanadiyyar ran mutumin.
Edafe ya bayyana cewa an kama mutum uku da ake zargi da aikata laifin kuma ana ci gaba da bincike.
- BBC Hausa