An kara tabbatar da Garba Bulangu a matsayin shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Jigawa

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa ta kara tabbatar da Garba Muhammad Bulangu a matsayin shugaban kungiyar ‘Yan Jaridu na kasa reshen jihar Jigawa.

Wannan dai na kunshe ta cikin wata sanarwa da uwar kungiyar ta kasa ta fitar a Abuja aka rabawa manema labarai ciki har da gidan radio Sawaba.

Sanarwar ta ce uwar kungiyar ta kasa ta samu rahoton zargin cewa kwamittin ayyuka na kungiyar a jihar Jigawa na ikirarin cewa wasu shugabannin kungiyar sun dakatar da shugaban kungiyar ‘yan jaridu na jihar Jigawa Garba Muhamma Bulangu bayan wani taro a ranar laraba 22 ga watan Nuwamba 2023. Sanarwar ta kara da cewa uwar kungiyar ta kasa Garba Muhammad Bulangu har gobe shine zababben shugaban kungiyar na jihar Jigawa wanda ya cika dukkanin wasu sharudan kungiyar don haka yana da dukkanin wasu goyon baya daga sakatariyar kungiyar ta kasa.

Comments (0)
Add Comment