Rundunar ‘yansandan Kasar nan ta ce ta kama wasu mutum biyu da take zargi da yunƙurin haifar da tarzoma a zaben gwamnan jihar Edo da ke gudanar a yau Asabar.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan ƙasar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar yau Asabar, ya ce ‘yansandan sun kama mutanen biyu masu shekara 43 da 41 a jiya Juma’a da maraice bayan da suka samu bayanan sirri cewa mutanen na shirin tayar da tarzoma a zaɓen na yau.
ACP Adejobi ya ce an kama su ne a mazaɓar Oredo, inda kuma bayan fara bincikarsu aka gano ƙananan bindigogin pistol ƙirar gida guda uku da wata babba guda ita ma ƙirar gida.
Ya ƙara da cewa ‘yansanda na ci gaba da riƙe mutanen biyu domin faɗaɗa bincike, inda ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
A yau ne dai al’ummar jihar Edo ke gudanar da zaɓen gwaman jihar.
Dama rundunar ‘yansandan ƙasar ta ce ta girke jamai’ai kusan dubu 35,000 domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben da ma bayan zaɓen.