Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta sanar da kama wasu mutane goma da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar nan.
A cewar wata sanarwa da DSP Shiisu Adams, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar nan ya fitar, an kama mutanen ne a kokarin da ake na yaki da aikata laifuka da kuma kare muhimman ababen more rayuwa a jihar nan.
A cewar Shiisu, uku daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne a Yalleman a yayin da ake gudanar da bincike kan zargin satar wasu kaya a cikin na’ura rarraba wutar lantarki da ke unguwar Gajo.
Ya bayyana cewa, mutane biyu da ake zargin sun fito ne daga garin Yalleman da ke karamar hukumar Kaugama, yayin da na ukun ya fito daga kauyen Hadin da ke karamar hukumar. Ya ce an kuma kama wani wanda ake zargin a yankin Mechanic da ke cikin garin Dutse, inda aka same shi da wasu konannin wayoyin lantarki da ake zargin an sace.