Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane bakwai da suka shiga zanga-zangar da akayi ranar Laraba a jihar biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na korar Gwamna Abba Yusuf.
Sawaba Radio ta ruwaito cewa kotun sauraron kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun soke zaben gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
Da yake yiwa manema labarai jawabi a yammacin Laraba, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Hussaini Gumel, ya ce an kama bakwai daga cikin masu zanga-zangar a Kano Line yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gidan gwamnati. Ya kuma bukaci mazauna jihar da su kasance masu kaunar zaman lafiya tare da bin doka da oda kasancewar ‘yan sanda tare da sauran jami’an tsaro sun dauki kwararan matakan tsaro domin dakile tabarbarewar rashin zaman lafiya a fadin jihar.