An kama wasu kayayyakin giya a wani yanki na karamar hakumar Hadejia

Kwamatin tsaro na karamar hakumar Hadejia daya kunshi gamayyar jami’an tsaro ya kama wasu kayayyakin giya a wani yanki na karamar hakumar.

Kayayyakin da suka hada da kwalaben giya da sauran kayan laifi, an same su ne bayan kwamatin ya kaddamar da wani sumame a wani gida da ake zaton ana aikata laifuka.

Shugaban karamar hakumar Hadejia Alhaji Abdukladir Umar ne ya yi bajakolin kayan a gaban manema labarai da malamai da sauran jami’ai.

Yace ta’ammali da giya haramun ne da ya saba da dokar jihar Jigawa.

Karamar hakumar Hadejia na kaddamar da irin wannan sumame lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da kakabe munanan ayyuka a cikin garin.

Babban limamnin masarauta Sheikh Yusuf Abdurrahman Yau, shugaban kungiyar JIBWIS na jihar jigawa da sauran malamai da kungiyoyin cigaban al’uma sun halarci taron. Tun da farko shugaban kwamatin Abdulkadir Usman daya ke jawabi yace sun samu bayanan sirri ne cewa ana aikata barna a yankin na Turarawa.

Comments (0)
Add Comment