Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta sanar da kama wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da zamba, aikata laifuka ta yanar gizo, fashi da makami, da sauran miyagun ayyuka a jihar.
Rundunar ta yi kame a ‘yan watannin nan, inda ta kwato motocin da aka sace, da babura, da sauran kayayyaki.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce an kama mutanen ne bisa kokarin jami’an rundunar.
DSP Adam a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan ya bayyana cewa, duk wadanda aka kama za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya yaba wa kokarin jami’an rundunar, ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa ‘yan sanda goyon baya a kokarin da suke na yakar miyagun laifuka. Don haka rundunar ta tabbatar da cewa a shirye ta ke ta yi aiki ba dare ba rana domin yakar miyagun laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.