An kama wasu da ake zargi da fashi da makami a jihar Jigawa

Rundunar yan sandan jihar jigawa ta kama wasu mutane da ake zargi da fashi da makami da kuma tsallakawa gidan mutane.

DSP Lawan Shiisu Adam kakakin rundunar ya bayyana haka a wata sanarwa da aikewa gidan radiyon sawaba jiya.

Yayi bayanin cewa sun aikata barnar ne da safiyar ranar 19 ga watan yuli, inda wadanda ake zargin su 5 suka tsaallaka gidan wani mutum dake unguwar G9 a Dutse babban birnin jiha.

A cewar sa wadanda ake zargin sun sace wata mota karar Honda Accord 2011 da bidiyo yar bango, da kwamfiyita da water hannu krar Redmi da sauran su. Kakakin yan sandan yace lokacin bincike wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa.

Comments (0)
Add Comment