Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da kama wata mata mai suna Rukayyah Amadu ‘yar shekara 20 bisa zargin kashe kishiyarta, Asiyah Amadu, bayan da ta watsa mata ruwan zafi sakamakon sabani da ya shiga tsakaninsu a kauyen Buju, karamar hukumar Dutse.
An garzaya da wacce aka kona zuwa asibitin Dutse don jinya, amma a karshe likitoci sun tabbatar da rasuwarta a ranar 4 ga Maris.