An kafa kwamitoci da za su binciki wasu manyan makarantun ilimi biyu bisa zargin karkatar da kudade

Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya kafa kwamitoci da za su binciki wasu manyan makarantun ilimin jihar biyu mallakin gwamnati bisa zargin karkatar da kudade.

Makarantun sun hada da Jigawa State Polytechnic Dutse da Kwalejin Ilimi da Nazarin Shari’a ta Jihar Jigawa dake Ringim.

Kwamitin binciken na kwalejin Dutse yana da tsohon kwamishinan ilimi Farfesa Haruna Abdullahi Birniwa a matsayin shugaba, sai kuma shugaban ma’aikatan jihar Jigawa Nura Muhammad Ubayi a matsayin sakataren kwamitin.

Kwamitin da aka dorawa alhakin binciken kwalejin ilimi da nazarin shari’a dake Ringim kuwa, an nada Farfesa Dalha Waziri a matsayin shugaba da Harisu Garba a matsayin Sakatare.

Sharuɗɗan kwamitocin biyu sun haɗa da sake duba shirye-shiryen ilimi na cibiyoyin don tabbatar da daidaitattun ayyuka tare da tabbatar da gaskiyar ko akasin haka na zarge-zarge daban-daban na rashin bin ka’idoji wajen gudanarwar kowace makaranta. Idan zamu iya tunawa dai SawabaFm ta gano cewa, gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan zargin karkatar da asusun tallafin ilimi, da kuma wasu almundahana da akayi a makarantun.

Comments (0)
Add Comment