Hana shigo da shanu da rakuma da tumaki da dabino da sauran kayan abinci daga Jamhuriyar Nijar din ya biyo bayan rufe iyakokin kasar da hukumomin Najeriya suka yi.
‘Yan kasuwa da masu safarar kayayyaki da dillalai sun ce suna asarar abin da samu don rufawa kan su asiri, hakan ce ta sanya suka yi kira da a sake tunani daga bangarorin da ke rikici da juna.
Yanzu haka dai yan Najeriya, masu sayar da kayayyaki da kuma masu amfani da kayayyakin sun ce suna fuskantar karanci abubuwan da ake shigo da su daga kasar ta Nijar sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.
A ranar 26 ga watan Yuli ne sojojin Nijar karkashin jagorancin Abdourahamane Tchiani suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a wani juyin mulki.
Hakan ce tasa ‘yan kwanaki kadan bayan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta lashi takobin mamaye kasar Nijar matukar gwamnatin mulkin sojan kasar ta gaza maido da tsarin dimokradiyya.
Kungiyar karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta kuma kakaba mata takunkumi daban-daban da suka hada da rufe kan iyaka da yanke wutar lantarki da dai sauransu. Sai dai sakamakon wani bincike ya nuna cewa miliyoyin ‘yan Nijar sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon killace kasar, yayin da su ma ‘yan Najeriya suka fara jin tasirin takunkumin, musamman a fannin samar da abinci mai dauke da sinadarin furotin.