An Gwangwaje Wata Sakandire Da Kyautukan Kayan Karatu

Wata kungiya mai fafutukar inganta ilimi tun daga tushe a Hadejia mai suna Give North Educatioon ta kai ziyara ga makarantar Sakandiren Gwamnati ta Sambo.

Ziyarar dai na daga cikin yunkurin da kungiyar take yi domin karfafawa dalibai da malamai gwiwa a fannin koyo da koyarwa.

Yayin ziyarar ne aka gudanar da jawabai a fannin muhimmancin ilimi, illar shaye-shaye da kuma tarbiyya.

Shugaban kungiyar Usman Nasir Isah ya mika kyautuka ga makarantar wadanda suka hada da allin, littafan rubutu da kuma al’kaluman rubutu.

A nasa jawabin shugaban makarantar Mal. Muhd Ibrahim wanda ya samu wakilcin Malam Muntari Abdullahi yayi godiya ga kungiyar tare kuma da shaida musu cewa zasu yi amfani da kayan ta hanyar da ya kamata.

Daliban makarantar kuwa da wakilinmu Nura Sabo Anku ya tattauna da su, sun bayyana jin dadinsu da jawaban da aka gudanar a yayin taron don yanzu sun gani tabbas taimakon ilimi ba sai gwamnati ba.

EducatioonHadejiaJigawa
Comments (0)
Add Comment