An gano gawarwakin mutane 28 da aka bindige a garin Nouna da ke arewa maso yammacin kasar Burkina Faso.
Wata kungiyar farar hula ta dora alhakin kisan kan fararen hula masu dauke da makamai da ke ikirarin cewa su mambobi ne na rundunar sa kai da ke samun goyon bayan gwamnati da ke yaki da masu ikirarin jihadi.
Gwamnati dai ba ta ce komai ba kan wannan ikirarin, amma ta ce tana gudanar da bincike.
Burkina Faso dai ta sha fama da tashe tashen hankula na tsawon shekaru 10 da ya raba kusan mutane miliyan biyu da muhallansu.
Sojoji sun kwace mulki a Burkina Faso a watan Janairun da ya gabata, inda suka yi alkawarin kawo karshen hare-hare, amma har yanzu ana ci gaba da tashin hankali.
Gwamnati ta ce an gano gawarwakin ne a ranakun 30 da 31 ga watan Disamba.
Ta yi Allah wadai da tashin hankalin tare da yin kira da a kwantar da hankula, har sai an kammala bincike.