An fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin kasar Rwanda

A yau ne al’ummar ƙasar Rwanda ke kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin kasar, inda ake kyautata zaton Shugaba Paul Kagame zai sake samun nasara a karo na huɗu.

Ya mamaye kowane sakamakon zabe tun lokacin da ya zama shugaban kasa a shekarar 2000, inda yake samun sama da kashi 90 na ƙuri’un da ake kaɗawa.

Rahotanni sun ce a zaben baya na 2017 ya samu kashi 99 cikin 100 na ƙuri’un da aka kada, wanda kashi 96 cikin 100 na wadanda suka yi rijista sun yi zabe, abin da ya sa manazarta ke ganin akwai lauje cikin naɗi.

‘Yan takara biyu ne kawai aka tabbatar da cewa za su fafata da shi; Frank Habineza na jam’iyyar Democratic Green Party, da Payimana Philippe ɗan takara mai zaman kansa.

Dukkansu sun tsaya takara a zaɓen 2017.

Wannan dai shine karo na 4 da Poul Kagame mai shekaru 66 ke kokarin komawa milkin kasar bayan shafe shekaru 24 yana jagorancin kasar karkashin mulkin demokradiyya.

Ya zama shugaban kasa tun a 1994 a karshen yakin basasar kasar wanda yayi sanadin rayuka sama da dunu 800.

A zaben na yau za a zabi yan majalisu 53.

Comments (0)
Add Comment