Rundunar ‘yan sandan jihar Borno a jiya ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu, Adamu Ibrahim da Bukar Wadiya bisa zargin kashe wata matar aure Fatima Alhaji-Bukar ‘yar shekara 24 a duniya.
Marigayar dake zaune a Dikechiri a unguwar Bayan Gidan Dambe a cikin birnin Maiduguri a jihar Borno.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Sani Kamilu, ya rabawa manema labarai a Maiduguri.
A cewarsa, wacce abin ya faru akan ta, tana auren Adamu Ibrahim, wanda shi ne babban wanda ake zargi da aikata laifin.
A cewar majiyar yan sanda, binciken farko da aka yi ya nuna cewa kafin faruwar lamarin, ma’auratan sun samu sabani a cikin gida kan zargin karin aure da mijin ke shirin yi.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro sunyi wa gidan da lamarin ya faru kawanya, a yayin bincike an gano wasu kayayyaki da suka hada da tabarya, jaka, igiya, da kafet cike da jini, wuka, da motar Honda a gidan da lamarin ya faru. Kakakin yan sandan ya ce babu wata shaida da ta nuna cewa an karya kofar gida kafin shiga, kuma mijin ne kawai ke da mabudin gidan.