Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta baiwa maniyyata fiye da dubu 2 a jihar wa’adin kwanaki 10 da su kammala biyan Naira miliyan 2 da dubu 919 na kujerun aikin Hajji ko kuma su fuskanci barazanar rasa kugerun a bana.
Babban sakataren hukumar Dokta Yusuf Yaqubu Alrigasiyu ne ya bayyana hakan yayin wani karin haske da yayi a wani gidan rediyo mai zaman kansa a jihar.
Alrigasiyu ya bukaci wadanda suka yi ajiya da su tabbatar sun kammala biyan kudin kafin ko kuma ranar 20 ga Afrilu.
Ya bayyana cewa za a maye gurbin kujerun ga duk wanda ya kasa kammala biyansa, kuma hukumar alhazai ta kasa ta umurci hukumar da ta mika dukkan kudaden da aka biya kafin ranar 22 ga watan Afrilu. Sakataren zartarwar ya tabbatar wa alhazan cewa jihar ta samu mafi kyawun masauki a kusa da masallacin Harami na Makkah, ya kuma bukace su da su halarci taron bitar mahajjata kan yadda ake gudanar da aikin Hajji yadda ya kamata.