An amince da dokar da za ta kawo ƙarshen kisa da saida naman karnuka

Koriya ta Kudu ta amince da wata sabuwar dokar da za ta kawo ƙarshen kisa da saida naman karnuka nan da shekarar 2027.

Dokar za ta kawo ƙarshen daɗɗiyar al’adar cin naman kare.

A ƙarƙashin dokar, za a haramta yanka wa da sayar da naman ƙarnuka da rarrabawa.

Masu sana’ar sayar da naman kare na iya fuskantar hukuncin shekara kusan uku a gidan yari yayin da waɗanda ke kiwon karnuka don cin namansu ko sayar da namansu na iya shafe shekara biyu a gidan yari.

Sabuwar dokar za ta fara aiki ne nan da shekara uku inda aka bai wa manoma da masu gidajen abincin da ke sana’ar damar sake sabuwar sana’a. Za su miƙa ƙudurinsu na sauya sana’a ga mahukunta a ƙananan hukumominsu.

Comments (0)
Add Comment