An ɗora laifin ɗaukewar wutar lantarki a faɗin Sri Lanka kan wani biri da ya yi kutse a wata tashar lantarki da ke kudancin birnin Colombo.
Sannu a hankali dai lantarki na komawa a faɗin ƙasar mai al’umma miliyan 22, inda aka fi bai wa ɓangaren lafiya da kuma tsaftataccen ruwan sha muhimmanci.
“Wani biri ne ya yi kutse ga babban layin ba da wutar lantarkin mu, abin da ya janyo ɗaukewar wuta,” kamar yadda ministan makamashi ya shaida wa manema labarai.
An fara samun ɗaukewar lantarkin ne da misalin karfe 11 na safe agogon ƙasar, abin da ya tilasta wa mutane da dama su koma dogaro da injunan bayar da hasken wuta.
Jami’ai sun ce za a shafe sa’o’i kafin wuta ta koma.
Mutane sun yi ta sukar hukumomi da kuma yin shaguɓe kan lamarin a kafafen sada zumunta.
“Biri ɗaya ya janyo ruɗani a faɗin Sri Lanka. Lokaci ya yi ne da za a sake yin nazari kan ababen more rayuwa?”, a cewar wani mai suna Mario Nawfal, kamar yadda ya rubuta a shafin X.