Jagororin mulki a Sudan sun sake ɗage zaman rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ƙarshe ta dawo da mulkin dimokuraɗiyya saboda saɓani da ake ci gaba da samu tsakanin sojojin.
An ci gaba da tattaunawa cikin dare wanda ya mayar da hankali kan yarjejeniyar da aka shirya rattaɓa mata hannu a yau Alhamis.
Sudan ta shiga cikin rikicin siyasa tun watan Oktoban 2021, lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin shugaba Omar al Bashir a 2019 wanda ya shafe tsawon shekaru yana mulki.
Bayan nan, kazamar zanga-zanga ta biyo baya, inda aka kashe ɗaruruwan mutane tare da jikkata wasu da dama a tsawon shekara ɗaya da rabi da ya gabata.
A watan Disamban bara, sojojin suka amince kan wani tsari na sake miƙa mulki ga gwamnatin farar hula.
Sai dai an kasa ci gaba da tattaunawa, sakamakon rashin jituwar da aka samu kan haɗewar sojojin ƙasar da kuma dakarun sa-kai, karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar mulkin Sudan Mohamed Hamdan Daglo.
Kakakin tattaunawar ya ce har yanzu sun kuduri aniyar cimma matsaya da sojojin.
Ɓangarorin na fatan yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe za ta ba da damar sake buɗe baitil-malin ƙasar da Tarayyar Turai da kuma Amurka suka rufe tare da taimakawa tattalin arzikin ƙasar da ya shiga tasku.