Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta ɗauki sabon matakin soke takardar izinin zama ɗan ƙasa ga ƙarin wasu ƴan ƙasar da ake zargi da hannun a cikin ayyukan ta’addanci ko neman hargitsa ƙasar.
Sabon matakin da shugaban majalisa mulkin sojan ƙasar ya ɗauka a jiya ya shafi wasu ƴan Nijar guda biyu na kusa da hamɓararren Shugaban Ƙasa Mohamed Bazoum.
Wannan shi ne karo na uku da gwamnatin mulkin sojan Nijar ke ɗaukar irin wannan mataki inda zuwa yanzu ta soke takardar izinin zama ɗan ƙasa ga ƴan Nijar kusan 20 akasarinsu makusantan Bazoum ne.