An ƙaddamar da kudin kariya ga ƴan jarida da masu fafutukar ƴancin amfani da yanar gizo

Tun bayan zamowar intanet ga amfanin mutane gama gari a shekarar 1989, kawo yanzu amfaninta na ƙara ƙaruwa ga mutane ɗaiɗaiku da ƙungiyoyi da kuma kuma gwamnati.

Amma sai dai amfanin nata na tattare da hadari ga ƴan jarida da wadanda suke aiki domin kare hakkin ɗan Adam da kuma masu fafutukar ganin mutane sun ci moriyar wannan cigaba da dan Adam ya samu a duniya.

Yan jarida dake aiki tukuru wajen bankado badaƙala don fito da su fili saboda a ɗauki mataki na samun kansu a cikin hadarin da yake razana ga rayuwar su ko ya yi musu cikas yayin gudanar da aikinsu.

Don haka ƙungiyar Paradigm Initiative (PIN) da hadin gwuiwar wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da gidauniyoyin taimako na ƙasa da ƙasa suka tallafa wajen samar da wannan kundi.

Kundin dai an kaddamar da shi ta yanar gizo a jiya wanda ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai da masu kare hakkin dan Adam da sassan nahiyar Afrika.

Wannan kundi dai ana kiransa da suna #AYETA wadda kalma ce da ta samo asali daga harshen Yarbanci da take nufin Sulke.

Wannan kundi ya kunshi babi-babi kamar haka;

Bayani kan yancin amfani da yanar gizo

Bayani kan matakan tsaro da kariya a yanar gizo daga masu kutse ko zolaya

Batun toshe yanar gizo da sauransu.

Wannan kundi dai ‘Gbenga Sesan da Bonface Witaba ne su kayi ƙoƙarin samar da shi, duk da yake dai a matakin farko yake amma yayin kaddamarwar an bayyana cewa nan gaba za a sake faɗaɗa shi zuwa wasu harsunan don ya kai ga mutane masu yawan gaske.

Ga masu son ganewa idonsu wannan kundi ko sauke shi (download) har ma su turawa abokan aikinsu sai su shiga www.africaayeta.africa ko kuma a aika da tambaya zuwa hello@ayeta.africa

Digital RightsHuman RightsParadigm Initiative
Comments (0)
Add Comment