Mutuwar fararen hula ciki har da yara a harin jirgi mara matuki na kasar Amurka jiya a Kabul, babban birnin Afghanistan, ya jawo suka.
Amurka tace ta kashe ‘yan kunar bakin waken ISIS dake shirin kai hari a filin jiragen saman Kabul. Sai dai, an gano cewa jirgin mara matuki ya kuma kashe fararen hula 10, da shekarunsu ya kama daga 2 zuwa 40.
Kazalika, an harba rokoki da dama zuwa filin jiragen saman Kabul, kwana guda kafin karewar wa’adin janye dakarun Amurka daga Afghanistan.
Fadar Amurka, wacce ta tabbatar da harin, tace ba a samu tsaiko ba wajen kwashe dakarun kasarta, inda ta kara da cewa an yiwa shugaban Amurka Joe Biden bayani dangane da harin roka na baya-bayannan da aka kai da safe kan filin jirgin saman Hamid Karzai dake Kabul.
Wani jami’in Amurka ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kakkabo wasu daga cikin rokokin.