Amsar da na fadawa Trumph lokacin da ya tambayi dalilin da yasa nake kashe Kiristoci – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ta kaya tsakaninsa da takwaransa na Amurka Donald Trump, yayin da ake tsaka da rikicin manoma da makiyaya a kasarnan, inda yace Trump ya zargi gwamnatinsa da kuntatawa kiristoci.

Wannan dai na zuwa ne a gabar da shugaban ke yiwa ministoci da sauran manyan mukarraban gwamnatinsa kaimi wajen kare manufofi da kuma nasarorin da gwamnatin tasa ke samu.

Kalaman shugaban na zuwa ne, yayin bitar kwazon ministoci na kwanaki biyu da aka shirya, wanda ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaba Buhari yace yayin da Trump yayi masa tambaya kan kisan Kiristocin, a karin hasken da yayi masa cewa, rikicin bai shafi kabilanci ko addini ba.

BuhariNigeriaTRUMPH
Comments (0)
Add Comment