Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Kadada 12,000 Na Amfanin Gona A Jigawa

Ambaliyar ruwa ta lalata Kadada 12,000 na amfanin gona a jihar Jigawa, kayan amfanin gonar da suka gamu da iftila’in ambaliyar sun hadar da Shinkafa Rogo da Ridi da kuma Dawa a kauyuka 9 na yankin karamar hukumar Malammadorin jihar.

Kansila mai wakiltar mazabar Tashena a karamar hukumar Alhaji Yunusa Bulama ne ya bayyana hakan a yau Lahadi yayin da yake jawabi ga Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kaugama da Malammadori Alhaji Maki Yalleman, yayin da ya ziyarci yankin.

Alhaji Yunusa Bulama ya ce, a shekaran jiya Juma’a ne iftila’in ambaliyar ya afku a yankunan da suka hadar da Tashena da Kadumunbari da Hadyan da Azumu da Kadumantudu da Dowawa da Dososo da Allahyayi da kuma Unguwar-Jamaare.Haka kuma ya kara da cewa kimanin kadada 8,000 na shinkafa aka yi asara sakamaon ambaliyar da kuma kadada 4,000 na Rogo da kuma sauran da suka hadar da Ridi da Dawa.

A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Alhaji Hussaini Birnin-Kudu, ya ce an raba wa mutanen yankin buhuna guda 5,000 wadanda za su zuba yashin domin datse gabar kogin Hadejia da ke yankin.

Shi kuwa dan Majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Kaugama da Malammadori Alhaji Maki Yalleman, jajanta wa al’ummar yankin ya yi ta re da yi musu Addu’ar Allah ya mayar musu da abinda ya fi wanda suka rasa.Alhaji Maki Yalleman ya kara da cewa, makasudin zuwansa shi ne domin duba irin asarar da aka samu a yankin, tare da cewa zai aiko musu da gudunmawa nan gaba kadan.

Auwal Hassan Fagge (WBM)

Comments (0)
Add Comment