Kungiyar kare haƙƙin yara ta Save the Children ta ce ambaliya a ƙasashen yammacin Afirka ta yi sanadin raba mutum kusan 950,000 da muhallinsu tare da hana yara samun ilimi.
Rahoton ƙungiyar ya ce kusan mutum 649,184 ambaliyar ta raba da gidajensu a Nijar, yayin da a Najeriya kuma ta raba mutum 225,000 da gidajensu.
Ambaliyar ta kuma raba mutum 73,778 da muhallinsu a kasar Mali, a cewar Save the Children.
Hukumomin Najeriya sun ce ambaliyar ta shafi jihohi 29 cikin 36 na ƙasar, galibi a arewacin ƙasar inda ta yi sanadin mutuwar mutum kusan 200.
Ambaliyar ta kuma shafe gonaki da dama tare da tafiya da gidaje da dabbobi.