Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, a matsayin ranar hutu domin bikin cikar kasarnan shekaru 60 da samun yancin kai.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ayyana hutun a madadin gwamnatin tarayya.
Babbar sakatariya a ma’aikatar cikin gida, Georgina Ehuriah, ta sanar da haka cikin wata sanarwar da ta fitar yau a Abuja.
- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Aregbesola ya taya daukacin yan Najeriya murnar cikar kasarnan shekaru 60 da yancin kai, inda ya tabbatar musu da jajircewar gwamnatin wajen habaka jin dadi da tattalin arzikin kasarnan.
Da yake taya yan Najeriya murna gudanar da bukukuwan yancin kan lafiya, ministan ya tunatar da cewa wadanda suka kwatowa kasarnan yanci, duk da banbancin addini, kabila da yare, sun hada kan su domin samun yancin kan kasa.