Alamu na nuni da samun ɗaukewar wutar lantarki a jihohin Kano, da Jigawa, da kuma Katsina yayin da ƙungiyar manyan ma’aikatan wutar lantarki da haɗin gwiwar kamfanoni (SSAEAC) suka fice daga ofishin kamfanin samar da wutar lantarki na (KEDCO) yau Alhamis a kano.
Ƙungiyar wacce ke samun goyon bayan ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta ƙasa (NUEE), ta ɗauki matakin ne sakamakon ƙin amincewa da kamfanin na KEDCO ya yi da wani sharaɗi da ɓangarorin biyu suka amince da su a baya.
Dakta Baba Gana, Mataimakin Sakatare Janar na manyan ma’aikatan wutar lantarki a Arewa, ya yi ƙarin haske kan batutuwa da dama da suka haɗa da rashin biyan kuɗaɗen fansho na watanni 79, da kin biyan haraji na (PAYE) na watanni 80, da kuma bashin 2019 zuwa 2023, da kuma wani ɓangare na 2022.
Buƙatun ƙungiyar sun kuma haɗa da biyan ƙarin albashin ma’aikata na 2020, 2021, da 2023, da basussukan 2019, da kuma alawus na sufurin ma’aikata, da haƙƙokin ma’aikatan da suka yi ritaya.
Dakta Gana ya bayyana cewa za su ci gaba da ƙin shiga aikin har sai lokacin da hukumar za ta warware waɗannan matsalolin.