Babban Alkalin kotun kasar nan John Tsoho, ya ce kawo yanzu akwai akalla kararraki dubu 128 da aka shigar a babbar kotun tarayya dake Abuja wadanda har yanzu baa kai ga yanke hakunci ba.
Babban alkalin ya bayyana haka ne a jawabinsa a wani zama na musamman kan shirye-shiryen shiga sabuwar shekara jiya a Abuja.
Yayin da yake jawabi ga wani bangare na alkalai a taron, babban alkalin ya bayyana cewa an shigar da dubban kararrakin laifuka tsakanin Satumbar shekarar 2020 zuwa watan Yuni 2021.
Ya ce akwai shari’o’in fareren hula guda 40,822, da shariun laifuka guda 30,197, da kararrakin cin zali guda 35,563 da kuma wasu kararraki 20,258 dake da alaka da hakkokin doka a gaban kotun a karshen wannan shekarar.
Mai shari’a Tsoho ya bayyana cewa an shigar da kararraki da yawa, kuma takardun alkalan sun cika da yawa sakamakon cikas da cutar corona ta kawo.