Akalla ‘yan Nijeriya 31,800,000 ne ke fama da matsalar karancin abinci sakamakon matsin rayuwa

Akalla ‘yan Nijeriya miliyan 31,800 ne ke fama da matsalar karancin abinci sakamakon tabarbarewar tsaro da cire tallafin man fetur wanda ya haifar da matsi da tsadar rayuwa.

Wannan adadi a cewar shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ya zarta adadin mutanen da suka fada matsananciyar yunwa a irin wannan lokaci a bara da ya kai mutane miliyan 18,600.

Wasu bayanan hadin gwiwa da hukumomin kasa da kasa na abinci da lafiya da kuma na agaji suka fitar a jiya Laraba, sun ce halin matsananciyar yunwar da ake ciki a Nijeriya lamari ne mai ba da tsoro.

Rahoton ya ce matsalar tsaro ta hana manoma da dama iya gudanar da harkokinsu na noma, lamarin da ya haddasa karancin abinci, yayin da a bangaren guda hauhawar farashi ke hana mutane iya sayen kayan abincin da ake shigowa da su daga kasashen ketare. Ƙungiyoyin sun ce matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cire tallafin man fetur ya taka muhimmiyar rawa wajen haddasa matsalar karancin abinci da kuma tsadarsa ta yadda magidanta da dama ba sa iya ci su koshi.

Comments (0)
Add Comment