Akalla fursunoni 3,590 ne ke cikin gidajen gyaran hali a fadin kasar nan ke jiran hukuncin kisa, kamar yanda Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta kasa (NCoS) ta bayyana.
Mai magana da yawun hukumar, Mataimakin ACC Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan a yayin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, a yau Laraba a Abuja.
Ya ce adadin jimillar fursunoni a gidajen gyaran hali a fadin kasar ya kai dubu 84,741, wanda ya kunshi maza dubu 82,821 da mata 1,920, kamar yanda yake a ƙididdigar da aka fitar jiya Talata.
Kakakin ya bayyana cewa jimillar fursunonin da ke jiran shari’a sun kai 57,750, wanda ya kunshi maza 56,303 da mata 1,447.
Da yake bayani kan yanayin kowannensu, cewa fursunonin da aka yanke wa hukunci sun kai dubu 21,900, wanda ya kunshi maza dubu 21,519 da mata 381, yayin da aka yanke wa 1,501 hukuncin daurin rai da rai, wanda ya kunshi maza 1,478 da mata 23.
Jimillar fursunonin da ke jiran hukuncin kisa kuma sun kai 3,517 maza da mata 73, wanda ya kawo adadin zuwa 3,590.